Fiye da mutane 12 sun rasu a wani harin kunar bakin wake a Kabul | Labarai | DW | 30.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fiye da mutane 12 sun rasu a wani harin kunar bakin wake a Kabul

Wani dan kunar bakin ya tada bama-bamai a cikin jama´a da suka taru a wajen harabar ma´aikatar harkokin cikin gidan Afghanistan dake birnin Kabul, inda ya halaka akalla mutum 12 sannan fiye da 40 suka samu raunuka. Daga cikin wadanda harin ya rutsa da su har da jami´an ma´aikatar da ´yan sanda wadanda suka hadu a gaban wata kofa kafin su fara aiki. A halin da ake ciki kuma kungiyar Taliban ta yi ikirarin kai harin. A bana dai birnin Kabul ya fuskanci hare haren kunar bakin wake ciki har da wani harin bam da aka kai da mota a ranar 8 ga watannan na satumba, wanda ya kashe fararen hula 14 da kuma sojin Amirka su biyu. A cikin watanin baya-bayan nan dakarun da ke karkashin jagorancin kungiyar tsaro ta NATO da takwaronrinsu na Afghanistan na fuskantar tirjiya daga mayakan Taliban.