1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fito na fito tsakanin 'yan sanda da masu bore

Mohammad Nasiru AwalMarch 18, 2015

An yi hargitsi a lokacin bikin bude sabuwar cibiyar babban bankin Turai a birnin Frankfurt, inda mutane da yawa suka raunata.

https://p.dw.com/p/1Esgl
Frankfurt EZB Protest Blockupy
Hoto: Getty Images/DANIEL ROLAND

'Yan sanda da masu zanga-zanga sun yi taho mu gama a lokacin bikin bude sabuwar cibiyar Babban Bankin Turai da ke tsakiyar birnin Frankfurt na nan Jamus. 'Yan sanda sun yi amfani da feshin ruwa da kulake a kan masu boren da suka yi ta jifan jami'an tsaron da duwatsu. An kone motocin 'yan sanda da kuma shingayen da suka kakkafa. Mutane da yawa sun jikata daga bangarorin biyu, sannan 'yan sanda sun kame mutane da yawa. A dangane da bikin na bude sabuwar cibiyar Babban Bankin Turan an rufe makarantu da ke wannan unguwa, sannan an takaita zirga-zirgar ababan hawa. Ministan shari'ar Jamus Heiko Maas ya zargi masu boren da karya dokokin 'yancin yin zanga-zanga. Kakakin kungiyar Blockupy da ta shirya zanga-zangar Malte Fiedler cewa yayi:

"Mun shirya zanga-zangar hana bikin bude sabuwar cibiyar Babban Bankin Turan domin a garemu ba mu ga abin yin biki ba a lokacin da talauci ke karuwa saboda manufofin kudi na Bankin Turan da sauran hukumomin lamuni."