1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fitinar tsageru matasa a Faransa

Shugaba Nicolas Sarkozy na Faransa ya yi alƙawarin daƙile fitar tsageru dake tashin zaune tsaye a ƙasar.Jim kaɗan da dawowarsa daga wata ziyara a ƙasar Sin, Mr Sarkozy ya ziyarci Jami´an tsaron da aka jiwa raunuka a faɗan taho mu gama, a tsakanin su da tsagerun. A lokacin zanga-zangar rahotanni sun shaidar da cewa tsagerun, sun halaka ´Yan sanda biyu tare da jikkata wasu da dama. A wani lokaci nan gaba, Mr Sarkozy zai gana da Jami´an Gwamnatinsa don ɗaukar matakin daya dace akan tsagerun matasan. Rikicin dai ya samo asaline bayan da wasu matasa biyu su ka rasa rayukansu, a hatsarin mota daya haɗa da motar ´Yan sanda na ƙasar.An dai bayyana wannan zanga-zanga, a matsayin mafi muni a ƙasar, a tsawon shekaru biyu da su ka gabata.