Firimiyan Benin ya tsallake rijiya da baya
December 27, 2015Talla
Zinsou ya je garin Djougou da ke a yankin Arewa maso yammacin kasar ta Benin domin halartar wasu bukukuwa na Ganni da ake gudanarwa a duk watan Disamba na ko wace shekara a wannan yanki. Sai dai kawo yanzu ba'a gano musabbabin wannan hadarin jirgin mai saukar ungulu ba. Amma tuni aka soma bincike a kan lamarin. Wata majiya ce ta fadar shugaban kasar ta Benin ta tabbatar da wannan labari
A watan Yunin da ya gabata ne Shugaban kasar Yayi Bony Yayi ya nada Lionel Zinsou wanda yake da takardar zama dan kasar Faransa a matsayin Firaminista, kuma jama'a da dama na masa kallon wani wanda ka iya maye gurbin shugaban kasar a karshen wa'adin mulkinsa.