Firiministan Turkiya ya kafa majalisar zartaswa | Labarai | DW | 24.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Firiministan Turkiya ya kafa majalisar zartaswa

Sabon Firiministan Turkiya Binali Yildirim ya kaddamar da sabuwar majalisar zartarwa sa, kwanaki biyu bayan da shugaban kasar Racep Tayyip Erdogan ya bashi gabarar yin hakan.

Sabuwar majalisar wacce mafi yawancin ta ministocin da sune yanzu haka suka sake zama a mukaman su in ban da Firiministan daya sauka daga mukaminsa.

Sabuwar majalisar wacce take kunshe da masu goyan bayan Erdogan bayan da Ahmet Davutoglu ya yi murabus daga kujerarsa ta Firiministan, to sai dai sauye sauyen da ake tunanin samu sun zowa mutane da ban barakawai ganin bayyanar masu ra'ayin kawom sauyi basu da yawa a cikin majalisar.

Sabon Firiministan wanda ake masa kallon yana da alaka ta kut-da kut da Erdogan jam'iyyar AKP ta zabe shi ne a ranar Lahadin nan a matsayin shugaban ta wanda ya maye gurbin Ahmed Davutoglu sakamakon jayayyar shugabanci da shugaban kasar.