Firayim ministan China ya fara rangadi a Turai. | Labarai | DW | 02.10.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Firayim ministan China ya fara rangadi a Turai.

Wen Jiabao ya isa Girka a matsayin yanki na rangadin da yake yi a Turai.

default

Wen Jiabao

Firayim ministan China, Wen Jiabao ya isa birnin Athens na ƙasar Girka a yau, domin yin ziyarar yini biyu, wadda a yayinta Girka ke kyautata fatan samun taimakon ta da makoɗar tattalin arziƙinta. asar ta Girka dai na bukatar jari daga kasashen waje domin biyan bashin kudin da aka bayar domin ceto tattalin arzikinta daga durkushewar da ya yi-abin da ya tilasata mata daukar matakan tsuke bakin aljihu. Wannan ziyara ta Wen wani yanki ne na rangadin da yake yi a kasashen Turai.  A ranar Litinin ne ne idan Allah ya kaimu Fraministan na China zai zarce zuwa birnin Brussels na kasar Beljiyam inda za a gudanar da taro tsakanin China da Kungiyar Tarayar Turai. Daga nan kuma zai zo nan Jamus kana ya karasa zuwa kasar Italiya da kuma Turkiya.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Yahouza Sadissou Madobi