1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Firamiyan Isra’ila ya gana da Condoleeza Rice a birnin Washington.

A ziyarar aikin da yake kai wa Amirka, Firamiyan Isra’ila Ehud Olmert, ya gana da sakatariyar harkokin wajen Amirkan Condoleeza Rice a birnin Washington. Ba a dai ba da ƙarin haske kan tattaunawar da suka yi ba, amma ana zaton cewa batutuwan da suka yi musayar yawu a kansu, sun haɗa ne da rikicin Isra’ilan da Falasdɗinawa da kuma ce-ce- ku cen da ake yi kan batun makamashin nukiliyan Iran. A yau ne dai ake sa ran Olmert zai gana da shugaba Bush a fadar White House.