Firamiyan Isra’ila, Ehud Olmert, ya ce a shirye yake ya gana da shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas. | Labarai | DW | 16.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Firamiyan Isra’ila, Ehud Olmert, ya ce a shirye yake ya gana da shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas.

Firamiyan Isra’ila, Ehud Olmert, ya faɗa wa majalisar dokokin ƙasarsa, wato Kneset cewa, a shirye yake, kuma kai tsaye ya sadu da shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas, don tattauna batun farfaɗo da shawarwarin zaman lafiya tsakaninsu. Ehud Olmert ya yi wannan jawabin ne kwana ɗaya bayan wasu kafofin yaɗa labarai sun ari bakinsa yana mai cewar, duk yunƙurin da ya yi na shirya taro tsakaninsa da shugaban Falasɗinawan ya ci tura. A cikin jawabin da ya yi wa Kneset ɗin dai, Olmert ya kuma yi kira ga takwaran aikinsa na ƙasar Lebanon Fouad Siniora da ya amince da saduwa da shi don su yi shawarwarin share fagen wani taro da zai iya kasancewa tushen samad da zaman lafiya tsakanin ƙasashen biyu.