Firamiyan ƙasar Sin zai fara wata ziyara a nahiyar Afirka. | Labarai | DW | 14.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Firamiyan ƙasar Sin zai fara wata ziyara a nahiyar Afirka.

Firamiyanm ƙasar Sin, Wen Jiabao, zai fara wata ziyarar mako ɗaya a nahiyar Afirka tun daga ran asabar mai zuwa. Wata sanarwar da gwamnatin ƙasar ta bayar a birnin Beijing, ta ce Firamiyan zai ziyarci ƙasashen Masar, da Ghana, da Jumhuriyar Kwango, da Afirka Ta Kudu da Angola, da Uganda da kuma Tanzaniya ne a cikin mako ɗayan.

Masharhanta dai na ganin cewa, Sin na ƙarfafa hulɗoɗin dangantaka na nahiyar ta Afirka ne saboda matuƙar bukatar albarkatun ƙasa da kuma makamashi da take yi. A halin yanzu dai, Sin na samun kusan kashi ɗaya bisa uku na man fetur da take bukata ne daga nahiyar Afirka.