1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Firamiya Wen Jiabao na Sin ya gana da Angela Merkel a birnin Berlin

YAHAYA AHMEDSeptember 15, 2006

A ci gaba da ziyarar da yake yi a nan Jamus, Firamiyan ƙasar Sin, Wen Jiabao, ya gana da shugaban gwamnatin tarayya Angela Merkel da kuma shugaban ƙasa Horst Köhler a birnin Berlin. Inganta hulɗodin cinikayya tsakanin ƙasashen biyu na cikin muhimman batutuwan da shugabannin suka tattauna.

https://p.dw.com/p/Bty9
Shugaba Köhler da Firamiya Wen Jiabao a Berlin.
Shugaba Köhler da Firamiya Wen Jiabao a Berlin.Hoto: AP

Firamiya Wen Jiabao na ƙasar Sin ya fara ya da zango a nan Jamus ne a birnin Hamburg, inda ya halarci wani taron ƙasa da ƙasa kan tattalin arziki. Daga bisani ne kuma ya taso zuwa birnin Berlin. Firamiya Wen dai ya bukaci ya yi wannan tafiyar daga Hamburg zuwa Berlin ne da jirgin ƙasan nan mai bala’in sauri, wato InterCity Express, maimakon ya tafi a sama. Jirgin, na tafiyar kilomita ɗari 3 da ke tsakanin biranen biyu ne cikin minti 90 kawai.

Shugaban gwamnatin tarayya Angela Merkel da kanta ce ta zo tashar jirgin ƙasa ta Belin don ta tarbi Firamiyan na ƙasar Sin. Bisa tambayar da ta yi masa ko yaya ya ji da daɗin tafiya da jirgin ƙasan, Firamiya Wen ya ce ya gamsu ƙwarai da saurin jirgin da kuma yadda aka ƙayatad da shi. Yana kuma fatar Sin za ta iya samun fasahar ƙera irin wannan jirgin daga Jamus. Babu shakka wannan fatar, wani abin alfahari ne ga tattalin arzikin Jamus. Sai dai, kamfanoni da yawa na nan ƙasar na koke-koken cewa, sau da yawa, ’yan ƙasar Sin ɗin na ƙera kayyayakin jabu na samfurorinsu da suka shafe shekaru suna bincike a kansu, abin da ke karya farashin kayayyakin asalin a ƙasashen ƙetare. Game da wannan batun dai, Angela Merkel ta bayyana cewa:-

„Za mu yi tattaunawa mai zurfi a kan wannan matsalar, saboda duk masu sha’awar zuba jari a Sin, su sami tabbacin cewa, ba za a ƙware su ba. Tuni dai na sami labarin cewa, ’yan ƙasar Sin na begen karɓar baƙwancin masu zuba jari daga Jamus da hannu biyu-iyu.“

Ita dai Jamus, ita ce muhimmiyar abokiyar hulɗar Sin a nahiyar Turai. Ana kuma samun matuƙar bunƙasar cinikayya tsakanin ƙasashen biyu. Firamiya Wen Jiabao ma ya bayyana a cikin jawabin da ya yi a birnin Berlin cewa, a wannan shekarar cinikayya tsakanin Sin da Jamus z ata kai dola biliyan 80.

A tattaunawar da suka yi a ofishin shugaban gwamnatin tarayya dai, shugabannin biyu ba su taƙaita shawarwarinsu kan tattalin arziki kawai ba. Angela Merkel ta kuma takalo batun take hakkin maneman labarai da ake ta ƙara zargin mahukuntan birnin Beijing da shi. Shugabannin jam’iyyun siyasa da dama ne dai suka tofa albarkacin bakinsu wajen suka Sin da iza wuta wajen tantance labarai da kuma take hakkin ’yan jarida. Da take yi wa maneman labarai jawabi bayan tattaunawar da ta yi da Firamiya Wen Jiabao, Anngela Merkel ta bayyana cewa:-

„Na bayyana wa Firamiyan dalla-dalla cewa, waɗannan hakkokin, babu mai izinin take su, ko’ina kuma a duniya. Na kuma yi matashiya da wasannin Olympics da za a yi a birnin Beijing, inda na nanata masa cewa, bai wa maneman labarai cikakken ’yancinsu a wannan lokacin na da muhimmanci ƙwarai wajen cim ma nasarar wasannin. Za mu dai ci gaba da tuntuɓar juna a kan wannan batun.“

Shugabannin biyu dai sun kuma tattauna batutuwan da suka shafi harkokin siyasar ƙasa da ƙasa, a cikinsu kuwa har da rikicin da ake yi da Iran kan batun makamashin nukiliyanta. Kawo yanzu dai, Sin, a matsayinta na ƙasa mai kujerar dindindin a kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya, ta yi watsi da batun sanya wa Iran ɗin takunkumi. Game da matsayin da Sin ɗin ta ɗauka a kan wannan batun dai, Firamiya Wen Jiabao ya bayyana cewa:-

„Muna sha’awar ganin an warware rikicin makamashin nukiliyan na Iran, amma a namu ganin, takunkumi ba zai cim ma wannan burin ba. A daura da haka ma, sai a sami akasin sakamakon da ake niyyar samu. Sabili da haka ne muke ganin ya kamata a yi taka tsantsan, wajen ɗaukan irin waɗannan matakan. Tun da dai akwai fatar warware rikicin, to kamata ya yi mu ci gaba da yunƙurinmu na hannunka mai sanda.“

A kan tambayar ko Ƙungiyar EU za ta takalo batun soke takunkumin makaman da ta sanya wa Sin ɗin, idan Jamus ta karɓi ragamar jagorancin ƙungiyar a shekara mai zuwa, Angela Merkel ba ta ba da ciikakkiyar amsa ba. Cewa dai ta yi, wannan batun ba ya kan ajandar batutuwan da za a tattauna a kansu a halin yanzu a birnin Brussels.