Firaminsitan rikon kwaryar Somalia ya isa birnin Mogadishu | Labarai | DW | 29.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Firaminsitan rikon kwaryar Somalia ya isa birnin Mogadishu

Shugaban gwamnatin wucin gadin Somalia Ali Mohammad Gedi ya koma Mogadishu babban birnin kasar, inda rahotanni suka ce ya samu kyakkyawar maraba. Kafofin yada labaru sun rawaito cewar dubban mutane ne suka yi cincirindo akan titunan a lokacin da ayarin motocin Mista Gedi suka isa birnin na Mogadishu.Ya kai ziyara a tashar jirgin ruwan a cikin yanayi na tsauraran matakan tsaro. A halin da ake ciki dakarun gwamnati wadanda Ethiopia ke marawa baya, su ke iko da yankuna da dama na kasar da ke yankin kahon Afirka. Yayin da shigar sa a birnin ke zama wata alama ta nasara, ana fargabar yiwuwar barkewar fada. Domin mayakan gamaiyar kotunan Islama wadnda a halin yanzu suke birni Kismayo mai tashar jirgin ruwa, sun lashi takobin ci-gaba da yaki.