Firaminsitan Isra´ila Ehud Olmert na ziyara a Rasha | Labarai | DW | 18.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Firaminsitan Isra´ila Ehud Olmert na ziyara a Rasha

Shugaban Rasha Vladimir Putin da FM isra´ila Ehud Olmert sun gudanar da jerin shawarwari a birnin Mosko akan shirin wanzar da zaman lafiyar yankin GTT da kuma fito na fiton da ake yi game da aikace aikacen shirin nukiliyar Iran da KTA. Isra´ila ta yi watsi da ikirarin da gwamnatin Teheran ta yi cewa shirinta na nukiliya na samar da makamashi ne amma ba makamai ba. FM Olmert ya fadawa shugaba Putin cewa Rasha ka iya taimakawa a warware wannan takaddama. Wani batu da shugabannin biyu suka tattauna a kai shine makaman da Rasha ke sayarwa Iran da Syria. Isra´ila ta sha yin korfain cewa kungiyar Hisbollah ta yi amfani da makaman da aka kera a Rasha a yakin da suka gwabza a kudancin Lebanon. Ta ce watakila Iran da Syria ne suka turawa ´yan Hisbollah da wadannan makamai.