Firaministan Ukraine ya yi murabus | Labarai | DW | 10.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Firaministan Ukraine ya yi murabus

Firaministan Ukraine Arseny Yatseniuk ya mika takardarsa ta barin aiki a wani yunkuri na bada dama a girka sabuwar gwamnati a kasar.

Mr. Yatseniuk ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya yi ga al'ummar kasar ta gidan talabijin inda ya ke cewar ''na yanke shawara ta ajiya aiki a matsayina na firaministan Ukraine kuma ranar Talata 12 ga wannan watan zan mika takardar barin aiki a hukumance ga majaklisar dokokin.''

Tsohon firaministan dai ya ce sauka daga mukamin nasa na da nasaba da rikicin siyasa da ya dabaibaye kasar wanda ya ce wasu tsiraru ne da gayya suka haddasa shi don biyan bukatun kansu.

Wannan yanayi da aka shiga dai zai baiwa kawance jam'iyyun da ke dasawa da kasashen yamma damar kafa gwamanti wanda hakan ka iya yin sular samun bashi daga Asusun Bada Lamuni na IMF da aka yi niyar baiwa kasar tun a bara, matakin da tsohon firaministan ke adawa da shi.