Firaministan Sri Lanka Rajapakse ya yi shailar lashe zaben shugaban kasa | Labarai | DW | 18.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Firaministan Sri Lanka Rajapakse ya yi shailar lashe zaben shugaban kasa

FM Sri Lanka Mahinda Rajapakse ya yi shailar lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a jiya alhamis. To sai dai sakamakon wucin gadi da aka bayar ya nunar da cewa FM na gaban shugaban ´yan adawa Ranil Wickremesinghe da yawan kuri´u da bai taka kara ya karya ba. Shi dai FM Rajapakse ya kasance mai goyon bayan daukar matakan ba sani ba sabo akan ´yan tawayen Tamil Tigers. Hukumomin kasar sun ce zaben na jiya alhamis ya tafi cikin lumana ba tare da wani tashin hankali ba. To amma wani labarin da ya iso mana ya ce mutane da dama sun rasu a wani harin bam da aka kai kan wani masallaci dake gabashin kasar ta Sri Lanka a yau juma´a. Hukumomin kasar na zargin ´yan tawayen tamil Tigers da hannu a wannan hari. Su dai ´yan tsirarun kabilar Tamil sun kauracewa zaben shugaban kasar. Tsarin mulkin kasar ya haramtawa shugaba mai ci Chandrika Kumaratunga tsayawa takara a karo na uku.