Firaministan Somalia Ghedi ya yi roko da a kai musu dauki | Labarai | DW | 26.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Firaministan Somalia Ghedi ya yi roko da a kai musu dauki

Firaministan Somalia Ali Mohammed Ghedi ya yi kira ga kasashen duniya da suka kai musu dauki don tinkarar barazana ta karuwar aikin ta´addanci a kasar. FM ya yi roko da a ba su taimako don hana kungiyar al-Qaida samun gindin zama a Somalia. FM Ghedi yayi wannan kira ne bayan da sojojin sa kai na kotunan Islama suka fadada ikonsu bayan sun kwace birnin Kismayo mai tashar jiragen ruwa a ranar lahadi da ta wuce. Rahotanni sun shaidar da cewa an kashe mutane 3 ciki har da wani yaro mai shekaru 13 a duniya sakamakon fadan na baya bayan nan. Kotunan Islaman wadanda suka musanta duk wata alaka da al-Qaida sun ce sun kwace birnin na Kismayo ne don hana wata rundunar kungiyar tarayyar Afirka shiga kasar. Gwamnatin wucin gadin Somalia dake da mazauni a Baidoa ta zargi ´yan Islaman da daukar sojojin sa kai daga Eritrea, Pakistan da Yemen, abin da ya karya dokokin yarjejeniyar zaman lafiyar Somalia da aka kulla a Sudan.