Firaministan Palasdinu ya musanta dakatar da tattaunawar kafa gwamnatin hadaka | Labarai | DW | 17.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Firaministan Palasdinu ya musanta dakatar da tattaunawar kafa gwamnatin hadaka

Firaministan Palasdinawa Ismail Haniyeh ya musa cewa shugaban Palasdinawa Mahmud Abbas ya dakatar da tattaunawar kafa gwamnatin hada a yankin.

Haniyeh yace,an jingine tattaunawar ce saboda Abbas zai hakarci tarukan Majalisar Dinkin Duniya ne cikin wannan mako.

Tun farko a yau masu baiwa shugaban na Palasdinwa shawar sun sanarda cewa,an dakatar da tattaunawar saboda kungiyar Hamas mai mulki ta janye daga sharuddan yarjejeniyar kafa gwamnatin hadaka.

Haniyeh ya fadawa manema labaru cewa,sun shirya tare da Abbas cewa zasu ci gaba da tattaunawa da zarar Abbas din ya komo daga taron na Majalisar Dinkin Duniya.