Firaministan Nuzilan John Key ya yi Murabus | Labarai | DW | 05.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Firaministan Nuzilan John Key ya yi Murabus

A wannan Litinin din ce (05.12.2016) shugaban gwamnatin ta Nuzilan Key, ya yi murabus din mai cike da ba-zata ga jama'ar kasar yayin da yake cikin wa'adin mulkinsa na uku.

Fimanistan ya sanar cewa ya yi wannan murabus din ne bisa wasu dalillai da suka danganci na iyali. Ya ce wannan mataki ne mai wahalar gaske da bai taba daukan irinsa ba a rayuwarsa. Sai dai da yake magana kan wannan batu, jagoran jam'iyya mai mulki a kasar ta National Party Andrew Little cewa ya yi:

" Kaman kowa, nima wannan sanarwa ta murabus ta bani mamaki, kuma ina so in sanar da ku cewa mukamin firaminista nauyi ne mai wahalar gaske a kowane lokaci, wahala wajen tafiyar da shi, sannan kuma ga su kansu iyallan mutumin. Don haka ina mai jinjinawa John Key da ya sadaukar da lokacinsa ga wannan kasa tamu."

A ranar 12 ga watan nan na Disamba ne dai jam'iyyar ta National Party za ta yi zama domin sake zaben wani sabon firaministan kasar ta Nuzilan, wanda zai maye gurbin John Key wanda tuni ya ce zai kada tashi kuri'a ga ministansa na kudi idan zai nemi wannan mukami.