Firaministan Netherlands zai yi murabus | Labarai | DW | 30.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Firaministan Netherlands zai yi murabus

A yau ake sa ran Firaministan kasar Netherlands Jan Peter Balkanende zai mika takardar yin murabus ga sarauniyar kasar tare da kiran zabe cikin gaggawa.

Membobin gamaiyar jamyiun adawa dai sunyi murabus daga majalisa,cikin wani rikici akan yadda ministar kula da shige da fice ta kasar ta tafiyar da batun kasancewa yar kasa na yar majalisa Ayaan Hirsi Ali haifaffaiyar Somalia.

Tunda farko dai ministar Rita Verdonk ta soke zama yar kasa ta Hirsi Ali wanda yanzu haka take Amurka,bayan ta amince cewa,ta bada bayanan karya a lokacinda take ciki takardun neman mafaka a kasar.

Ana sa ran gudanar da zabe a watan Oktoba.