Firaministan Lebanon ya yi kira ga ´yan ƙasar da su taimakawa jami´an tsaro | Labarai | DW | 20.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Firaministan Lebanon ya yi kira ga ´yan ƙasar da su taimakawa jami´an tsaro

FM Lebanon Fuad Siniora ya zargi kungiyar Fatah al-Islam da kokarin ta da zaune tsaye a cikin kasar bayan musayar wutar da aka yi tsakanin sojojin sa kai na wannan kungiya da kuma sojojin gwamnati. A cikin wata sanarwa FM Siniora ya nunar da cewa kashe sojojin Lebanon da ´yan Fatah al-Islam suka yi wani babban laifi da aka tsara shi tun ba yau ba, wanda kuma ke zaman yunkuri da ke da hadarin jefa kasar cikin rudani. Yayi kira ga al´umar Lebanon wadanda suka shafe watanni da dama suna fama da dambaruwar siyasa da su marawa soji da dakarun tsaron Lebanon baya. Akalla mutane 19 ciki har da sojoji 11 da ´yan takifen Fatah al-Islam 7 da kuma farar hula daya aka kashe a fadan da ya barke a birnin Tripoli dake arewacin Lebanon.