Firaministan kasar Italiya ya yi murabus | Labarai | DW | 05.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Firaministan kasar Italiya ya yi murabus

Tun farko dai Matteo Renzi ya sha alwashin cewa idan har masu adawa da kawo sauyi ga kundin tsarin mulkin kasar da ya bukata suka yi rinjaye, to zai yi murabus daga mukaminsa.

Da yake magana jim kadan bayan sakamakon zaben da bai bashi nasara ba, Renzi ya ce: "Na yi bukatar kawo sauye-sauye a tsarin tafiyar da siyasar kasar ta Italiya da suka shafi majaliyasar wakillai, da batun jihohi da kuma majalisar tattalin arziki kasa, amma hakan ba ta samu ba, don haka dole in dauki wannan mataki."

Dan shekaru 41 da haihuwa Firaministan na Italiya mai murabus, da ya shafe kwanaki sama da dubu kan wannan mukami, zai mika takardar murabuns din sa ne a wannan Litinin din (05.12.2016) ga shugaban kasar ta Italiya Sergio Mattarella yayin  wani taron majalisar Ministoci.

Sai dai daga nashi bangare Beppe Grillo, babban mai adawa da Firaministan ya ce wannan ishara ce ga kowa, domin ba za a ci gaba da yi wa al'ummar karya ba, ba tare da an fuskanci sakamakon hakan ba.