1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Firaministan Iraqi ya maida Martani ga Amurka

August 23, 2007
https://p.dw.com/p/BuDP

P/M Iraqi Nuri al-Maliki ya maida martani da kakkausar harshe ga sukar da Amurka ke yiwa gwamnatin sa da gazawa wajen shawo kan tarzoma da kuma sasanta kan alúmar Iraqi. Nuri al-Maliki ya yi watsi da sukar yana mai cewa babu wanda yake da ikon sanyawa gwamnatin sa wadda alúma suka zaɓa wani ƙayyadadden lokaci. A hannu guda kuma shugaban Amurka George W Bush yayi kashedin cewa ficewar Amurka daga Iraqi ka iya haifar da yanayi irin wanda ya wakana a kudu maso gabashin Asia, bayan da sojojin Amurka suka fice daga Vietnam. Yayin da yake jawabi ga tsoffin sojoji a Missouri, Bush yace Miliyoyin jamaá fararen hula waɗanda basu ji ba basu gani ba, sun ɗanɗana kuɗar su a sakamakon ficewar da Amurkan ta yi daga Vietnam. Ya kuma jaddada goyon bayan sa ga P/M Iraqi Nuri al-Maliki wanda a yanzu ya sami kan sa cikin wadi na tsaka mai wuya.