1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Firaministan Iraƙi ya yi kira da ´yan siyasar Amirka da su koma cikin hankalinsu

Firaministan Iraqi Nuri al-Maliki ya yi watsi da kiran da wasu ´yan siyasar Amirka suka yi na a maye gurbinsa da sabon FM. A lokacin da yake magana a gaban wani taron manema labarai a birnin Bagadaza al-Maliki ya nuna fushinsa kai tsaye akan ´ya´yan majalisar dattawa na jam´iyar Demiocrat wato Hillary Clinton da Carl Levin, yana mai cewa bai kamata su rika yi kamar Iraqi ta su ce. Ya ce ya kamata su dawo cikin haiyacin su. FM na Iraqi ya kuma yi suka ga ministan harkokin wajen Faransa Bernard Kouchner wanda ya yi kira da a maye gurbin gwamnatin al-Maliki.