Firaministan Iraƙi al-Maliki ya yiwa majalisar dokoki a Bagadaza jawabi | Labarai | DW | 10.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Firaministan Iraƙi al-Maliki ya yiwa majalisar dokoki a Bagadaza jawabi

Firaministan Iraqi Nuri al-Maliki ya ce gwamnatinsa ta hana Iraqi fadawa cikin wani yakin basasa sannan ya sha alwashin cika alkwarin da ya dauka na sasanta ´yan shi´a masu rinjaye da kuma larabawa ´yan Sunni. A lokacin da ya ke kare matakin kara yawan dakarun Amirka a Bagadaza, Maliki ya fadawa majalisar dokoki cewa tashe tashen hankula a babban birnin na Iraqi ya ragu da misalin kashi 75 cikin 100. FM na Iraqi ya yiwa majalisar jawabi ne sa´o´i kalilan gabanin kwamandan Amirka a Iraqi Janar David Petraeus ya gabatarwa majalisar dokokin Amirka da rahotonsa akan Iraqi. Petraeus zai ba da kiyasin sa a dangane da manufofin shugaba GWB a Iraqi musamman a kan kara yawan dakarun Amirka a kasar.