Firaministan Habasha Zenawi ya gargadi Eritrea game da rikicin kan iyaka | Labarai | DW | 05.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Firaministan Habasha Zenawi ya gargadi Eritrea game da rikicin kan iyaka

FM Habasha Meles Zenawi ya gargadi makwabciyar kasarsa wato Eritrea da ka da ta kuskura ta dauki wani matakin soji akan sa. A wani jawabi da yayi ta gidan telebijin, FM Zenawi ya ce a shirye dakarun tsaron kasarsa suke su dauki duk matakan da suka wajaba don kare kasarsu. A cikin makonnin da suka wuce an yi ta samun hauhawar tsamari akan iyakar kasashen biyu. Tuni MDD ta yi kira a garesu da su nuna halin ya kamata kana kuma su guji abin da zai kai ga ba hamata iska a tsakani. A dangane da rikicin siyasa na cikin gida, an ci-gaba da gudanar da zanga-zanga a biranen Addis Ababa da Bahir Dar don nuna adawa da sakamakon zaben ´yan majalisar dokokin Habasha da ya gudana cikin watan mayu. Sama da mutane 40 rahotannin suka tabbatar da mutuwar su sakamakon rigingimun da ake yi a kasar a kwanakin nan.