Firaministan Girka zai gana da Merkel | Labarai | DW | 12.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Firaministan Girka zai gana da Merkel

A lokacin ganawar za a tattauna kan batutuwa da suka hadar da makomar Cyprus da batun 'yan gudun hijira ga batun tattalin arzikin kasar ta Girka.

Gwamnatin kasar Jamus ta bayyana cewa Firaministan kasar Girka Alexis Tsipras zai kai wata ziyara zuwa birnin Berlin fadar gwamnatin Jamus a wannan mako don tattaunawa da Shugabar gwamnati Angela Merkel kan batun 'yan gudun hijira da harkokin da suka shafi kudi a Cyprus da Girka.

Mai magana da yawun gwamnatin ta Jamus Ulrike Demmer ta bayyana a ranar Litinin din nan cewa Merkel za ta gana da Tsipras a ranar Juma'a. Ta ce za su tattauna kan batutuwan da suka hadar da makomar Cyprus da batun 'yan gudun hijira da dangantakar Kungiyar Tarayyar Turai da makociyar Girka daga Gabashi wato Turkiya, ga kuma batun tattalin arzikin kasar.