Firaministan Faransa de Villepin ya ce ba zai yi murabus | Labarai | DW | 04.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Firaministan Faransa de Villepin ya ce ba zai yi murabus

Firaministan Faransa Dominik de Villepin ya yi watsi da kirar da aka yi masa da yayi murabus, saboda zargin da aka yi masa cewa ya ba da umarnin gudanar da bincike a boye akan kudaden ajiyar ministan harkokin cikin gida Nicolas Sarkozy. FM ya ce ko da rana daya shugaban kasa bai taba ba shi wani umnarni na gudanar da wannan bincike ba. Wadannan kalaman da Villepin ya yi zasu wanke sunan shugaba Chirac, wanda ke shan suka dangane da rawar da ya taka a wannan batu. Da farko shugaban ´yan ra´ayin gurguzu Francois Hollande ya yi kira da shugaba Chirac da ya fito fili ya bayyana irin rawar da ya taka, kana kuma yayiwa gwamnatinsa garambawul.