Firaministan China Wen Jiabao ya kai ziyara birnin Harbin | Labarai | DW | 26.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Firaministan China Wen Jiabao ya kai ziyara birnin Harbin

FM China Wen Jiabao ya kai ziyara a birnin Harbin na arewa maso gabashin kasar, inda hukumomi ke kokarin tsabtace wani dagwalo mai guba da ya malala cikin kogi. Ziyarar ta Wen ta zo ne bayan da gwamnati ta tura wata tawagar bincike zuwa birnin na Harbin don gano dalilin da ya sa aka samu jinkiri na kwanaki 10 kafin a sanar da jama´a malalar sinadarin mai guba cikin kogin. A gobe lahadi ake sa ran maido da ruwan fanfo ga mazauna kimanin miliyan 4 a birnin. A kasar Rasha dake makwabtaka da yankin, hukumomi sun dauki matakan gaggawa don hana sindarin mai guba malala daga kogin Songhua zuwa yankin Khabarovski.