Firaministan Biritaniya yayi garanbawul a gwamnatin sa | Labarai | DW | 05.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Firaministan Biritaniya yayi garanbawul a gwamnatin sa

Faraministan kasar Biritaniya, Mr Tony Blair yayi garanbawul a gwamnatin sa, wanda hakan ya haifar da sauke ministocin harkokin cikin gida da na wajen kasar daga mukaman su.

Sauke Mr Jack Straw da kuma Charles Clark dai ya biyo bayan kaye ne da jam´iyyar Labo ta Mr Blair ta sha ne a zabubbukan kana nan hukumomi da aka gudanar a jiya alhamis.

Da yawa dai daga cikin masu fashin baki na ganin cewa jam´iyyar ta Labo tasha kashin ne, a sakamakon zargin gwamnatin ta Mr Blair da ake da gudanar da aiyuka na magudi.

An dai maye gurbin Jack Straw ne da sakatariyar ma´aikatar muhalli wato Margaret Beckett, kana John Reid kuma ya maye gurbin Charles Clark, a matsayin sakataren harkokin cikin gida.

Ya zuwa yanzu dai shima kann sa Mr Blair ya fuskantar matsin lamba daga yan jam´iyyar tasa ta Labo, na bayyana lokacin daya tsara sauka daga mukamin nasa.