Firaminista mafi ƙarancin shekaru a Birtaniya | Amsoshin takardunku | DW | 04.06.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Firaminista mafi ƙarancin shekaru a Birtaniya

Mr. David William Duncan Cameron an haife shi ne a birnin London shekaru Arba'in da ukku da suka shige.

default

Firaministan Britaniya David Cameron

An haife shi ne a birnin London ranar 09.10.1966. David shi ne na ukku daga cikin 'ya'yan Ian da Mary Cameron guda huɗu. Mahaifinsa ɗan kasuwa ne a kasuwar musayar kuɗi, kuma maifiyarsa ta yi aiki ne a matsayin maishari'a har na tsawon shekara talatin.

A lokacin da ya cika shekaru bakwai a duniya, mahaifansa sun tura shi zuwa wata mashahuriyar makarantar medil, wadda yawanci sai 'ya'yan tajirai da sarakuna ke halarta, cikinsu kuwa har da 'ya'yan Sarauniyar Ingila guda biyu Yarima Andrew da Edward. Daga nan ne kuma aka tura shi wata makarantar ta masu hannu da shuni da ake kira Eton.

Bayan ya kammala karatunsa a kwalejin Eton, kafin ya tafi zuwa Jami'ar Oxford inda ya karanta tattalin arziki da siyasa, Mr. Cameron, ya ɗauki tsawon wata ukku yana yiwa wani kamfanin jigilar jiragen ruwa aiki a Hong kong, kuma lokacin komowarsa gida ya bi ta hanyar jirgin kasane inda ya ratsa ta tsohuwar ƙasar Tarayyar Soviet zuwa cikin wasu ƙasashen gabashin turai.

Bayan ya kammala karatunsa na Jami'a da samun digiri nasahun farko, David Cameron da farko yana da burin zama ɗan jaridane ko kuma aikin Banki, to amma a ƙarshe ya nemi aiki a ofishin nazari da bincike na Jam'iyyar Conservative. Abokan aikinsa suna ganin mutum ne mai aiki tuƙuru da kuma cikakkiyar basira. A lokacin ne kuma ya yi aiki da manyan 'yan siyasar Jam'iyyar kamar tsohon kakakin jam'iyyar na fannin harkokin cikin gida Mr. David Davis. Haka kuma yana ɗaya daga cikin mashawartan tsohon Firaminista John Major a lokaci na ƙarshe da jam'iyyar ta ci zaɓe a Britaniya kawo yanzu.

A shekarar lokacin babban zaɓe na shekarar 1997 ne Mr Cameron ba tare da samun nasara ba, ya shiga takarar zama ɗan majalisar dokoki a mazaɓar Stafford. Shekaru huɗu bayan nan a babban zaɓen shekarar 2001, ya samu nasarar lashe takarar cinye mazaɓar Witney a gundumar Oxfordshire.

House of Commons Großbritannien

Zauren majalisar dokokin Birtaniya.

Shigarsa majalisar ke da wuya nan da nan sai matsayin Mr. Cameron ya riga samun ci-gaba-dai-gaba-dai, inda yai aiki a kwamitin harkokin cikin gida na Majalisar. Daga nanne sai tsohon shugaban Jam'iyyar Mr. Michael Howard ya bashi aiki a ofishin tsarawa da nazarin manufofin jam'iyyar. Kuma a lokacin zaɓen shekarar 2005 shine ke da dawainiyar tsara manufofin jam'iyyar a lokacin zaɓen. To amma jam'iyyar bata yi nasara ba.

To a bayan da Michael Howard ya sauka daga jagorancin jam'iyyar bayan da suka gaza cinye zaɓen 2005, sai David Cameron ya tsaya a takarar maye gurbin uban gidansa. Kuma duk da cewa ba mutane da yawa suka sanshi ba, to amma lokacin taron shekara na Jam'iyyar ya samarwa kansa farin jini yayin da yayi wani jawabi mai kyatarwa, kuma aka zaɓeshi sabon shugaban Jam'iyyar.

Bayan zaɓensa shugaban jam'iyyar, a lokaci guda kuma ga gwamnatin Labour na fama da baƙin jini a tsakanin al'ummar ƙasa, Mr. Cameron ya samun farin jini musamman a tsakanin kafofin watsa Labarai. Yayi alƙawarin wanke shunin da ya dagula harkokin siyasar ƙasa, tare da yin kira ga jam'iyyarsa da ta yi watsi da munufarta na yin ɗari-ɗari ga tarayyar turai.

Mr. Cameron, yana da yara ƙanana guda biyu da kuma ukku dake kan hanya, tare da mai ɗakinsa Samantha. Ɗansu na farko Ivan an haifeshine marili kuma Allah ya karɓi ransa a shekarar bara.

Ɗan shekaru Arba'in da ukku da haihuwa Mr. David William Duncan Cameron ya zama Firiminista mafi yaranta a tarihin Britaniya tun bayan Robert Banks Jenkinson, Hakimin birnin Liverpool, shekaru ɗari da casa'in da takwas da suka shige.

Mawallafi: Sani Dauda

Edita:Ahmad Tijjani Lawal