Fira da mataimakin ministan tsaron Iraqi | Siyasa | DW | 06.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Fira da mataimakin ministan tsaron Iraqi

Game da raɗe-raɗin da ke ta yɗuwa na cewa nan da shekara ɗaya dakarun ƙetare za su janye daga Iraqi ne, Björn Blashke, wakilin gidan rediyon WDR a birnin Amman na ƙasar Jordan, ya yi fira da mataimakin ministan tsaron Iraqi Raus Noor Shawys, don jin ra'ayin gwamnatinsa a kan wannan batun.

Masu zang-zanga a Iraqi

Masu zang-zanga a Iraqi

„A nawa ganin dai, kafin ƙarshen shekara ta 2006, dakarun Iraqi za su iya kula da kusan rabin harkokin tsaro a ƙasar su da kansu.“

Wannan dai ita ce fatar da mataimakin ministan tsaron Iraqi, Raus Noor Shawys ke yi wa ƙasarsa. Kawo yanzu dai, dakarun Iraqin ba sa iya yin wani ɗauki su kaɗai ba tare da kasancewar wani rukunin rundunar sojin Amirka tare da su ba. Sai zuwa ƙarshen wannan shekarar ne ake sa ran cewa cibiyar hafsan hafsoshin sojin Iraqin za ta kafu sosai. Shi dai mataimakin ministan tsaron ƙasar Shawys ya bayyana cewa:-

„Abin da muka fi bai wa muhimmanci a wannan shekarar, shi ne samun cibiyar hafsan hafsoshin sojin Iraqi, wadda muike sa ran cewa goshin ƙarshen shekara ta 2006, za ta iya kulawa da duk wani ɗaukin da rundunar Iraqin za ta yi.“

Tun shekara ta 2004 ne dai aka fara kafa sabuwar rundunar soji ta ƙasar Iraqin. Kawo yanzu dai, an sami bataliyoyi 10, waɗanda ko wacce daga cikinsu ke ƙunshe da sojoji dubu 7 da ɗari 5 zuwa dubu 9, duk da cewa dai har ila yau ba dukkkansu ne suka sami horo da kuma makaman da suka dace ba. Wannan kuma na ɗaya daga cikin dalilan da ke sa ba sa iya karawa da mayaƙan `yan tawayen ƙasar.

Mafi yawan sojojin dai yara ne samari, waɗanda kuma ba su taɓa zuwqa bakin daga ba, a daura da `yan tawayen, waɗanda su yaƙin ya zame musu jiki. Kamar dai yadda Shawys ya bayyanar, kusan kashi 90 cikin ɗari na `yan tawayen, wato manyan hafsoshin soji ne na Saddam Hussein. Sabili da haka ne a halin yanzu, ma’aikatar tsaron ke duk iyakacin ƙoƙarinta, wajen ganin cewa ta bai wa sabuwar rundunar sojin duk wani irin horon da ya kamata sojojin wannan zamanin su samu, inji mataimakin ministan. Kazalika kuma, za a ba su darussa kan tafarkin dimukraɗiyya, don su fahimci cewa, aikinsu kare jama’ar ƙasar, amma ba wani shugaba mai mulkin kama karya ba.

A halin yanzu dai, rundunar sojin Amirkan da abokan burminta da suka girke dakaru a Iraqin tare da wasu ƙasashen NATO, waɗanda ba su girke dakaru a Iraqin ba, kamar dai Jamus, sun ce sun horad da manyan hafsoshin sojin Iraqin dubu 12, tare kuma da wasu fararen hula, waɗanda za su yi aiki ƙarƙashin ma’aikatar tsaron ƙasar. Mataimakin ministan tsaron Iraqin dai, ya kyautata zaton cewa, Jamus za ta ci gaba da ba da tata gudummowa wajen horad da hafsoshin Iraqin kamar yadda take yi yanzu a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ko kuma a nan cikin gida.

Wannan furucin dai ya bambanta da wanda shi ministan tsaron Iraqin, Dulyami da kansa ya yi, inda ya bayyana cewa, ƙasarsa ba za ta dogara kan taimakon Jamus wajen horad da dakarunta ba.