Fillon ya zama dan takarar adawa na Faransa | Siyasa | DW | 28.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Fillon ya zama dan takarar adawa na Faransa

Tsohon Firaministan Faransa Francois Fillon ya zama dan takarar jam'iyya mai ra'ayin rikau a zaben shugaban kasa da ke tafe a shekara mai zuwa bayan ya doke Alain Juppe a zaben fidda gwani.

Francois Fillon ya kasance dan hakin da aka raina a zaben fidda da gwani na jam'iyyar Les Republicains ta kasar Faransa, saboda ba shi da kazar-kazar da karfin fada a ji a fagen siyasar kasar. Amma kuma dattaku da  tawali'u da sauye-sauyen da ya yi alkawarin yi sun sashi rikedewa i zuwa zakaran da Allah ya nufa da cara.

A zagayen farko na zaben fidda gwani na jam'iyyar ta masu ra'ayin rikau ya zo na daya ba zato ba tsammani, lamarin da ya bashi damar yin waje da 'yan takara da dama ciki har da tsohon shugaban kasa Nicolas Sarkozy. Hasali ma dai goyon bayan da ya samu daga tsaffin 'yan takarar ya sa Fillon samun rata mai yawa a fafatawar da suka yi a zagaye na biyu da Alain Juppe wanda shi ma tsohon Firaminista ne. A jimlance dai Francois Fillon ya lashe Kashi 66,5% na kuri'un da aka kada , yayin da Alain Juppe ya tashi da kashi 33,5%. Tuni ma Juppe da ya sha kaye ya yi wa takarar Les Republicains a zaben watan Afirilu barka da arziki.

"Ina taya Francois Fillon murnar samun nasara da gagarumin rinjaye. Ina jadadda kyakyawar hulda da girmamawa da ke tsakaninmu. Zan bashi hadin kai 100% a yakin neman zabe. Sannan ina masa fatan gudanar da yakin neman zabe lafiya tare da samun nasara a watan Mayu 2017."

Kididdigar jin ra'ayin jama'a da aka gudanar a Faransa ta nunar da cewar Francois Fillon zai zarta sauran 'yan takara yawan kuri'u a zagayen farko na zaben shugaban kasa, inda zai iya tashi da kashi 26% na kuri'un da aka kada. Yayin da Marine Le Pen ta jam'iyyar Front National ta masu kin jini baki zata biya masa baya da kashi 24% na kuri'u a zaben 23 ga watan Afirilu. Sai dai kuma tsohon Firaministan Fillon zai iya yi wa Le Pen kintinkau a zagaye na biyu sakamakon goyon baya da zai samu daga bangarorin da suka sha kaye ciki har da jam'iyyar Socialiste da ke rike da mulki a halin yanzu.

Sai dai Francois Fillon ya ce hakar jam'iyyar masu ra'ayin rikau ba zai cimma ruwa ba, matikar bai samun hadin kan kowa da kowa ba, ciki kuwa da Alain Juppe da ya kayar a zaben fidda gwani.

"kamar yadda na fada tun da farko ina so in bayyana wa Alain Juppe irin girmamashi da nake yi, da kuma irin gadara da nake yi da shi wajen taimakamin a wannan gaggwarmaya da zan fara na kawo karshen gwamnati da ke kan mulki. "

Shi dai Francois Fillon mai shekaru 62 da haihuwa ya rike mukamin minista so da dama a Faransa kafin ya zama Firaminista karkashin gwamnatin Sarkozy daga shekara ta 2007 zuwa 2012. Gwanarsa a fagen siyasa ita ce tsohuwar Firaministar Birtaniya Margaret Thacher. Hasila ma dai ya yi alkawarin rungumar salon sauye-sauyen da ta gudanar a lokacin da rike madafun iko, inda baya ga tsuke bakin aljuhu, zai rage yawan ma'aikatan gwamnati tare da tsawaita shekarun aiki kafin yin ritaya. Bugu dakari kuma ya sha alwashin kwaskware dokar nan da ke baiwa masu auren jinsi damar daukar rikon 'ya'ya da ba nasu ba.

Shi dai Francois Fillon yana da aure da kuma 'ya'ya biyar. Sannan mai sha'awar tseren motoci ne.

 

Sauti da bidiyo akan labarin