Filin jiragen saman birnin Brussels ya soma aiki
April 3, 2016Filin jirgi da ke a matsayin na farko a kasar ta Beljiyam ya kasance a rufe tun bayan tagwayen hare-haren da birnin na Brussels ya fuskanta a ranar 22 ga watan Maris wanda ya yi sanadiyar rasuwar mutane 32. Tuni dai jirgi na farko ya tashi a dazu-dazun nan da wajejen karfe daya da minti 40 na rana zuwa birnin Faro a Kudancin kasar Portugal dauke da mutane 60 zuwa 70 acikinsa, sannan wasu jiragen guda biyu masu zuwa Turin da kuma Athenes, za su tashi a wannan rana, yayin da ake jiran wasu jiragen guda uku da za su sauka a filin jirgin na Zaventem.
Filin jirragen saman na Zaventem ya yi kira ga matafiyan da su isa filin jirgin awoyi uku kafin tashinsa, kuma za su zo ne a mota domin jirgin kasa ko motocin bus-bus masu zuwa filin jirgin basu soma aiki ba kawo yanzu.