Fifa ta yi barazana dakatar da Nageriya | Labarai | DW | 02.07.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fifa ta yi barazana dakatar da Nageriya

Fifa ta ɗebawa hukumomin Nageriya wa'adin ƙwanaki ukku domin su dawo akan matakin da suka ɗauka na janye ƙungiyar wasannin ta Super Eagles daga fagen wasannin ƙwallon ƙafa

default

Shugaban FIFA Joseph "Sepp" Blatter

Hukumar wassannin ƙwallon ƙafa ta duniya wato Fifa ta yi barazana dakatar da ƙasar Nageriya daga wasannin ƙwallon ƙafa na ƙasa da ƙasa , idan har gwamnatin ƙasar  bata dawo akan matakin da ta ɗauka na janye ƙungiyar yan wassan Super Eagles ba  daga fagen wasannin na tsawon shekara biyu kafin nan da ranar litinin.

Hukumcin dakatarwa dai da ƙungiyar ta FIFA zata ɗauka akan Nageriya ya haɗa da soke kuɗaɗen tallafin da hukumar ke baiwa ƙasar da dakatar da ƙungiyar wassannin ta ƙasar sanan kuma da haramtawa duk wani alƙalin wasannin ƙwallon ƙafa na Nageriya aikin alƙalancin gasar ƙasa da ƙasa ta ƙwallon ƙafa.

yanzu haka dai hukumar ta FIFA ta sanar da cewa zata tura wani wakilin ta a ranar litinin mai zuwa  a ƙasar ta Nageriya domin tattaunawa da hukumomin akan wannan badaƙala da ta kuno kai.

Mawallafi  Abdourahamane Hassane

Edita         Halima balaraba Abas