Fifa ta gabatar da rukunin farko na ′yan takararta | Labarai | DW | 12.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fifa ta gabatar da rukunin farko na 'yan takararta

Hukumar zabe ta Fifa ta bayyana mutane biyar da ta amince da takararsu daga cikin mutanen da suka aza takara a zaben shugaban Fifa na watan Febairu shekarar badi

Hukumar zabe ta Fifa ta tantance takarar mutane biyar daga cikin jerin wadanda suka aza takarar neman shugabancin hukumar da za a yi a watan Febairu mai zuwa. Hukumar ta tabbatar da sahihanci takarar mutanen biyar ne a lokacin wani zama na musamman da ta gudanar a wannan Alhamis.

'Yan takarar da hukumar ta amince da su kawo yanzu sun hada da yarima Ali na Jodan, da Jerome Champagne dan kasar Faransa , da Tokyo Sexwale na Afirka ta Kudu.

Sai dai hukumar ta yi watsi da takarar Bility dan kasar Laberiya a yayin da ta jingine binciken takarar Michel Platini dan Faransa har sai bayan kammala wa'adin matakin dakatar da shi da hukumar ta yi.

A ranar 26 ga watan Febairu shekarar badi ne dai za a gudanar da zaben sabon shugaban hukumar ta Fifa wanda zai maye gurbin Sepp Blater wanda hukumar ta dakatar da shi bayan bankado zargin cin hanci da karbar rashawa a cikin hukumar ta Fifa