1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

FBI ta karya doka wajen sauraron hirarrakin jama´a ta wayar tarho

March 10, 2007
https://p.dw.com/p/BuQ6
Kungiyoyin kare hakkin jama´a a Amirka sun yi tir da hukumar ´yan sandan ciki wato FBI bayan ta amsa cewar ta take dokokin zaman jama´a ionda ta yi amfani da dokar kishin kasa don sauraron hirarraki ta wayar da karanta sakonni e-mail da kuma samun bayanai na ajiya bankunan ´yan kasar. Wani bincike da ma´aikatar shari´a ta yi ya gano cewar hukumar FBI ta take doka har sau 22 ciki har da neman bayanai ba bisa ka´ida na wasu kamfanonin wayar tarho guda 3. Babban atoni na Amirka Alberto Gonzales ya ce ba da gangan FBI ta aika wannan laifi ba. Wakilan jam´iyar democrats a majalisar dokoki sun sha alwashin gudanar da bincike akan bayanan da ma´aikatar shari´ar ta bayar. Bayan hare haren 11 ga watan satumba na shekara ta 2001 aka kafa dokar ta kishin kasa a matsayin wata dokar yaki da ta´addanci.