1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fata kan kafa gwamnatin Jamus

December 5, 2017

Akwai yuwuwar samun mafita kan kafa gwamnatin Jamus ta gaba saboda jam'iyya ta biyu mafi girma a kasar ta nuna shirin shiga kawance kafa gwamnati ta gaba.

https://p.dw.com/p/2olTU
Berlin Statement Martin Schulz zu möglichen Koalitionsverhandlungen (picture-alliance/AP Photo/M. Schreiber)
Hoto: picture alliance/AP Photo

Jagoran jam'iyyar SPD wadda take matsayi biyu wajen girma a kasar Jamus ya amince da shirin fara tattaunawa da jam'iyyar CDU ta shugabar gwamnatin Angela Merkel bisa matakin kafa sabuwar gwamnati ta gaba.

Jagoran jam'iyyar Martin Schulz ya tabbatar da cewa za a fara tattaunawar idan taron jam'iyyar na wannan makon ya rantaba hannu kan matakin. An gaza kafa sabuwar gwamnatin ta Jamus, tun bayan zaben watan Satumba, sakamakaon rashin cimma matsaya tsakanin jam'iyyar CDU mai mulki da kuma jam'iyyar FDP da kuma Greens mai kare muhalli.