1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fashin jirgin Sudan

Tanko Bala, AbdullahiAugust 27, 2008
https://p.dw.com/p/F5qp
Jirgin saman Fasinja kirar Boeing 737 wanda aka yi fashin sa bayan da ya tashi daga Nyala zuwa Khartoun a ƙasar SudanHoto: AP

Yan ƙungiyar tawayen yankin Dafur waɗanda suka yi fashin jirgin saman Sudan sun sako dukkan fashinjoji 95 dake cikin jirgin, sai dai kuma sun cigaba da yin garkuwa da maákata da kuma matuƙan jirgin.


Shi dai jirgin ƙirar Boeing 737 mallakar kamfanin zurga zurgar jiragen sama na Sun Airline ya tashi ne daga garin Nyala dake yankin Dafur zuwa Khartoum babban birnin ƙasar Sudan ɗauke da fasinjoji kimanin ɗari ɗaya yayin da wasu mutane biyu na ƙungiyar yan tawayen SLM dake Dafur suka karkata akalarsa. Tilas dai jirgin ya sauka a ƙauyen Kufra dake yankin Sahara a ƙasar Libya bayan da matuƙin jirgin ya shaidawa hukumomi cewa mai ya kusa ƙare masa.


Hukumomin Libyan sun tabbatar da cewa an sako dukkanin fasinjoji dake cikin jirgin, sai dai yan tawayen na cigaba da garkuwa da matuƙan jirgin da kuma maaíkata, bugu da ƙari sun kuma riƙe wasu yan sanda biyu na ƙasar Masar da mutane biyu yan ƙasar Habasha da kuma wasu yan Uganda su biyu. Ana dai cigaba da tattaunawa da masu garkuwar domin ganin an sako dukkanin ragowar maáikatan jirgin su shida tare da umartar

Waɗanda suka yi fashin jirgin su miƙa kan su.


Tun farko dai waɗanda suka yi fashin jirgin sun jaddada buƙatar ƙarawa jirgin mai domin wucewa zuwa Paris. Kakakin gwamnatin Sudan Abdul Hafiz Abdulrahim yace yan tawayen na ƙoƙarin neman mafaka ne a Faransa. Kamfanin dillancin labaru na ƙasar Libya ya ruwaito cewa matuƙin jirgin ya sanar da hukumomi cewa masu garkuwar yan ƙungiyar reshen SLM ne na yan tawayen Dafur wadda ke ƙarƙashin jagorancin Abdelwahid Mohamed Nur suna kuma buƙatar saduwa ne da shugaba nasu a birnin Paris.


Sai dai kuma ɓangaren na Abdelwahid Mohammed Nur ya nesanta kansa da yan fashin jirgin, yana mai cewa ba yan ƙungiyarsa bane. A waje guda kuma wani yanki na ƙungiyar yan tawayen ta SLM ɓangaren Minni Arcua Minnawi wadda a shekarar 2006 ta sanya hannu akan yarjejeniyar sulhu da gwamnatin Sudan, tace daga cikin fasinjojin dake cikin jirgin , akwai jamián ta bakwai waɗanda suka haɗa da wakilai uku dake cikin gwamnatin wucin gadi ta lardin Dafur. Ƙungiyar tace tana iya matuƙar bakin ƙoƙari domin tuntuɓar su a cewar wani babban jamiín ta Mohammed Bashir.


A halin da ake ciki gwamnatin Sudan ta yi kira ga hukumomin Libya su kama mutanen da suka yi fashin jirgin su kuma mika su gare ta, tana mai baiyana cewa wannan tamkar aiki ne na taáddanci yan tawayen suka aikata.