1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fashewar wasu abubuwa a Addis Ababa ta kashe akalla mutum 4

Akalla mutane 4 sun rasu sannan fiye da 40 sun jikata a fashewar wasu jerin abubuwa a Addis Ababa babban birnin kasar Habasha. ´Yan sanda sun bayyana abubuwan guda 9 da suka fashe da cewa wani aiki na bata gari to amma ba su bayyana wadanda ke da hannu a ciki ba. Abubuwan sun fashe ne a cikin wasu gine gine ofis guda biyu da wurin shan gahawa da wata tashar bas sai kuma wasu da suka fashe a cikin motocin safa 3 da kuma a karkashin wata gada a yankuna dabam dabam na birnin. Tun bayan zaben da aka gudanar bara wanda ake cecekuce akai a kasar ta Ethiopia, ake yi ta samun fashewar abubuwa a birnin na Addis Ababa.