Fashewar bututun mai a Nijeriya | Labarai | DW | 26.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fashewar bututun mai a Nijeriya

Kimanin mutane 260 suka halaka yayinda suke kokarin kwasar man fetur a wani bututu man fetur daya fashe a birnin Lagos a Nigeria.

Hukumar agaji ta Red Cross ta sanarda cewa wasu kusan 60 kuma sun samu kuna iri dabam dabam yayinda zafin wuta da hayaki sun kawo cikas ga aiyukan ceto dimbin jamaa da gobarar ta rutsa dasu.

Kungiyar ta Red Cross tace hadarin ya rutsa har da mata da yara kanana wadanda suka je kwasar ganimar mai a bututun da ya fashe a Agbule Egba.