1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fashewar bama-bamai a Iraƙi

November 25, 2007
https://p.dw.com/p/CSwt

´Yan sanda a birnin Bagadaza sun ce wani bam da aka ɗana cikin wata mota ya fashe a kusa da wani asibiti, inda ya halaka mutane 9. Harin wanda aka kai a unguwar Bab al-Muazzam dake arewacin babban birnin na Iraqi ya kuma jikata mutane 30. A wani harin na daban kuma wani bam da aka ɗana a gefen hanya ya fashe lokacin da sojojin Iraqi suke wucewa inda ya halaka faran hula daya sannan mutane 8 suka ji rauni. Waɗannan hare haren na aukuwa ne duk da raguwar tashe tashen hankula a faɗin ƙasar ta Iraqi baki ɗaya bayan an kara yawan sojojin Amirka.