Fashewar bam a Pakistan | Labarai | DW | 12.03.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fashewar bam a Pakistan

An sake samu fashewar bam a ƙasar Pakistan bayan wasu hare haren ƙunar baƙin wake.

default

Wata makaranta a Pakistan

Rahotanin daga ƙasar Pakistan sun ce an ƙara kai wasu sababin hare hare da yammacin yau a birnin lahore dake a yankin gabashin ƙasar.

Harin wanda ake kyautata zaton cewa yan ƙungiyar alƙaida ne suka kai shi har yanzu baá san yawan adadin mutanen da suka rasa rayukansu ba.

Daman dai tun can da farko Mutane a ƙalla guda 39 suka mutu  a cikin jerin wasu hare hare guda biyu da aka kai akan wasu motocin sojojin ƙasar Pakistan a birnin  Lahore .Wanda ke kan iyaka da ƙasar India,

hare haren wanda yan ƙungiyar Taliban ne suka yi ikararin kaisu,su ne  na biyar da aka kai a cikin wannan mako,bayan wanda aka kai a ranar litinin da ta gabata  inda mutane 13 suka mutu.

A ciki wata sanarwa da ya bayyana ministan harakokin waje na ƙasar ta Pakistan Shah Mehmood  ya yi Allah wadai da hare haren ya na mai cewa bazasu taɓa barin yan ta'adar ba su cimma ɓurinsu.A yan kwanakin baya baya nan dai dakarun ƙasar na Pakistan da sjojin Amurka sun ɗaɗa kai farmaki a yankin arewa ma so yammaci na ƙasar inda nan ne sansanin yan ƙungiyar na Taliban.Ƙungiyar dai ta yan Taliban na Afganistan ta yi gargadin cewa za ta cigaba da kai farmaki na ƙunar baƙin wake  akai akai  idan har dakarun  ƙasahen na Pakistan da na Amurka suka cigaba da neman su ruwa jalo

Mawallafi : Abdurahamane Hassane Edita : Abdullahi Tanko Bala