1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fasahar kirkirar manhajar kwamfuta a Kenya

Yusuf Bala Nayaya
January 11, 2017

Masu kirkiran manhajar kwamfuta a Kenya sun sake fasalin sababbin abubuwan da suke kirkira a dakin kimiyya na Nailab da ke birnin Nairobi.

https://p.dw.com/p/2VcMC
Kenia Bloggers Association of Kenya
Hoto: DW/J. Mielke

A kasar Kenya wani matashi mai suna  Joshua Mutua ya kirkiro da wata manhajar kwamfuta ta Apps mai suna Kejahunt, da ke taimakawa mutane masu neman gidan haya su sami gidaje cikin sauki ba tare da matsalar dillalai ba, godiya ta tabbata ga wata cibiyar rainon fasaha a birnin Nairobi mai suna Nailab da ke taimaka wa irin wadannan matasa.

Steve Walli ya kasance mutum da ke farin ciki bayan samun muhalli da yake iya biyan haya ba tare da takura ba a birnin Nairobin Kenya. Yakan yi tattali na abin da ke shigo masa bayan kauce wa dillali na samar da gidaje, godiya ta tabbata ga manhajar kwamfuta ta Apps din mai suna Kejahunt da Joshua Mutua ya kirkiro bayan fiskantar matsaloli a baya.

"Mun yi tunanin cewa ya kamata a samu hanya ta samun gidajen haya cikin sauki saboda zamba cikin aminci da ake samun dillalai na aikatawa, musamman a nan Nairobi, don haka muka yi tunani na fito da harkar a kwamfuta a yi ta a fili."

Sauya fasahohi don amfanin al'umma

Ita dai wannan manhaja ta Kejahunt da Joshua Mutua ya kirkiro ta samun bunkasa bayan sanya hannu na kwararrun fasahar kwamfuta a cibiyar rainon fasaha ta Nailab da aka kafa a shekarar 2010 bisa jagorancin Sam Gichuru bayan nazari da ya yi na cewa akwai bukatar tallafa wa hazikan matasa masu fasaha amma ba sa samun tallafi.

"Mun fara Nailab bayan da muka gano cewa akwai matasa fasihai, sai dai suna aiki su kadai don haka muka samar da wata cibiya da za su hadu su yi aiki tare su sami abin da suke bukata, wanda idan su kadai ne ba za su iya samun hakan ba."

Videostill Africa on the Move Amanuel Abrha und Eskinder Mammo
Amanuel Abrha da Eskinder Mammo 'yan kasar Habasha da su ma suka kirkiro manhajar kwamfuta don amfanin AfirkaHoto: DW

Cikin horo na watanni shida  da cibiyar Nailab ke ba wa matasa sukan sauya fasahohinsu zuwa abin da al'umma za ta amfana. Da fari dai bunkasa fasahar ne burin cibiyar, amma yanzu bayan fitar da fasahar zuwa kasuwa cibiyar na da kashi 10 cikin 100 na abin da aka samu na riba. Abin da suke amfani da shi da bunkasa aiyuka a fadar Joshua Mutua makirkirin manhajar Kejahunt.

"Daya daga cikin kalubale da muke fiskanta a shirin da muke da shi na zama na fadada aikinmu zuwa Mombasa da Kisumu da Eldoret. Muna bukatar kiyasin Dala 5000 don wannan aiki, amma har yanzu ba mu iya tattara wannan kudi ba."

Dogaro da sabbin wayoyin salula

Da yawa al'ummar kasar ta Kenya dai na dogara ne da wayoyin hannu samfurin Smartphones a wuraren aiki ko a gida, akalla miliyan 30 cikin miliyan 43 na 'yan Kenya na amfani da su. Ana amfani da su wajen yin sayayya ko kasuwanci, sai dai amfanin wannan wayoyi sun fi gaban nan.

 

Gwamnatin Kenya dai ta ware tallafi na Dala miliyan daya da dubu dari shida don samar da cibiyoyi na bunkasa fasaha 30 a shekara ta 2016, baya ga bibiya da tallafi ga wadannan cibiyoyi don su bunkasa. Sai dai baya ga gwamnati akwai bukatar al'umma su shigo wannan fage don zuba jari ba wai kawai a zuba jari na ajiyar kadarori ba kamar filaye da gidaje da dai sauransu.