1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Farmakin sojin Amurka a Iraqi

March 18, 2006
https://p.dw.com/p/Bv4n

Hukumomin sojin Amurka sun baiyana farmakin haɗin gwiwa da suka kaddamar tare da dakarun Iraqi a kan mayaƙan sari ka noƙe a garin samarra, da cewa ya ƙara kaifafa basirar dakarun Iraqin na ɗaukar gagarumin nauyin gudanar da shaánin tsaron kasar. Janyewar sojojin Amurka daga Iraqin dai ya dogara ne ga yadda dakarun Iraqin suka sami kwarewa da za su iya ƙarbar ragamar shaánin tsaron kasar. Dakarun sojin Amurkan dana Iraqi sun cigaba da kai farmaki a biranen Bagadaza da samarra domin murƙushe abin da suka kira ɓurɓushin yan takife a ƙasar Iraqi. A cewar wani kwamandan sojin Amurka Lt Col Edward Loomis yace farmakin da suka kai ta jiragen sama wanda shi ne mafi girma a tsawon shekaru uku da suka gabata ya cimma nasara ba tare da wata turjiya ba.