1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Farmakin Israila a Gaza

May 17, 2007
https://p.dw.com/p/BuLP

Jiragen yaƙin Israila samfurin F-16 sun yi luguden wuta a kan Hedikwatar gudanarwa ta ƙungiyar Hamas a birnin Gaza. Maaíkatan ceto sun kai ɗauki zuwa ginin wanda luguden wutan ya ragargaza domin kai waɗanda suka ji rauni zuwa Asibiti. Harin dai ya maida yankin gidan jiya bayan lafawar arangama tsakanin Hamas da Fatah. Rahotanni sun ce a ƙalla mutum guda ya rasa ran sa wasu mutanen goma sha biyu kuma suka sami raunuka bayan ɗauki ba daɗi tsakanin Hamas da Fatah a lokacin wata janaiza a yankin Rafah. A sakamakon wannan yamutsi shugaban palasɗinawa Mahmoud Abbas ya ɗage ziyarar da ya shirya kaiwa zuwa Gaza domin tattaunawa da P/M Ismaila Haniya domin ceto gwamnatin haɗin kan ƙasar. A waje guda kuma shugaban Masar Hosni Mubarak ya buƙaci Palasɗinawan su dakatar da zubar da jini a tsakanin su, yana mai cewa haramun ne su riƙa zubar da jini a junan su. A tsawon shekaru Masar ke ƙoƙarin shiga tsakani domin sasantan Palasɗinawa da Israila.