Farkon azumin watan Ramadan | Labarai | DW | 13.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Farkon azumin watan Ramadan

Saɓanin Taraya Nigeria, Jamhuriya Niger, da Lybia, da su ka fara azumin watan Ramadan tun jiya, a yau ne mafi yawan ƙasashe muslunci na dunia su ka daujki azumin farko.

A ƙasar Indonesia da ta fi yawan muslmi a dunia, an fara azumin na shekara bana cikin halin juyayi, a sakamakon girgiza ƙasar da ta abku a jiya laraba, wada kuma ta hallaka a ƙalla mutane 10.

A ƙasar Bangladesh gwamnati ta bayyana dokar rage parashen kayan masarufi, albarkacin watan mai tsarki, da kashi 20 cikin ɗari.

Kazalika, a kussan dukan ƙasashen larabawa, a yau ne a ka fara gudanar da ibadar wattan ramadan.

A Irak da ke fama tashe-tahen hankula dakarun Amurika sun bayyana aniyar sako pirsinoni masu yawa a cikin wannan wata.

A nasu ɓangare, ƙasashen Marroko da Senegal, da kuma yan ɗarikar Schi´a, na Iran da Irak sun yanke shawara fara azumin gobe juma´a.