Fari a Afirka: Fargaba ta yunwa da kishirwa
Ba ruwan sama ba girbin amfanin gona, Afirka na fama da matsalar fari mafi muni a gwamman shekaru, abin da ke zama barazana ga mutane miliyan 14, musamman a kasar Habasha inda lamarin yafi muni.
Dakon ruwan sama
Jarkoki na ruwa sun bushe babu ko da digo daya na ruwan sha a ko'ina. Kasar Habasha ta ga fari mafi muni cikin shekaru 30, inda ta shafe tsawon watanni ba ruwan sama. Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane miliyan 10 na bukatar agajin abinci. Sai adadin kuma zai ninka. Haka wannan lamari yake a wasu kasashen na Afirka.
An samu asara da dama
Mafi yawan 'yan Habasha na rayuwa a wajen birane. Dabbobin da suke da su na tallafa wa iyalansu baki daya ne. Lokaci na karshe da aka ga ruwan sama shi ne lokacin watan Ramalana a cewar wani makiyayi a yankin Afar. Amma watan na Ramalana ya wuce tun a Yuli. Tun daga wancan lokaci babu ruwan sama , babu ruwan sha, babu ciyawa, dabbobi na mutuwa.
Yara na cikin hadari
Wannan fari na tuna wa al'ummar Habasha halin yunwa da aka tsinci kai a shekarar 1984 inda mutane miliyan daya suka rasu. Kasar yanzu na cikin matsalar rashin abinci, Yara da ke zama wadanda matsalar tafi shafa a cewar mahukuntan na Habasha su 400,000 ne maza da mata ke fama da tamowa abin da ya sanya bukatar su ga likita.
Sauyin yanayi na El Nino ya haifar da zafi
A kasar Zimbabuwe sauyin yanayi sakamakon sauyin teku da iskar bazara ta sanya ba a samu masara me kyau ba saboda sauyin da ake kira EI Nino, bin da ya jawo fari a Zimbabwe. A wasu sassa na duniya irin wannan sauyi na EI Nino na yin sanadi ne na ambaliya
Ta iya tsayawa kan kafafu?
Wannan saniya ta gaji yadda ba ta iya tsayawa a kan kafafunta. Ma'aikatan gona a Masvingo na kokari na ganin ta tsaya kan kafafunta hudu ta ci gaba da tafiya. Ruwan sama da kasar ta Zimbabuwe ke samu ya ragu da rabi a shekarar 2015 idan aka kwatanta da shekarun da suka shude, hakan ya sanya kasa ta bushe.
Kogi ya kafe
Bisa al'ada a wannan wuri mutum ba ya iya tsayawa ko ma zama saboda cikin kogi ne na Black Umfolozi. Amma wannan hanyar ruwa da ke a Arewa maso Gabashin Durban a Afirka ta Kudu ta kafe. Mazaunan wannan yanki kan haka karamar rijiya a nan don samun ruwa, hakan ne kuma ke taimaka musu dan ci gaba da rayuwa.
Fari ya haifar da hauhawar farashi
A Malawi wacce ita ma ke fama da fari, a kasuwar babban birnin kasar Lilongwe, kayan masarufi kamar masara farashinta ya tashi. Girbi da aka yi bai yi kyau ba don haka dole a shigo da kayan abinci daga ketare saboda karancinsu . Masu karamin karfi na fama wajen sayen kayan abincin saboda tsada.