1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargabar Turai kan sabon salon yakin IS

Gazali Abdou Tasawa
November 29, 2016

Kasashen Turai sun bayyana fargabarsu dangane da sabon salon yakin da Kungiyar IS ta fito da shi a Iraki inda take amfani da jirage marasa matuka na Drone wajen kai hare-haren ta'addanci. 

https://p.dw.com/p/2TRv7
Niger französischer Drohnen-Hangar
Hoto: Getty Images/AFP/P. Guyot

Kasashen Turan sun bayyana fargabarsu a game da yiwuwar fuskantar hari a cikin kasashensu, hare-hare kungiyar ta IS ta wannan sabon salo na dana bam ga jiragen marasa matuka. Tuni ma dai mahukuntan kasar Faransa suka gargadi sojojinsu da su yi taka tsan-tsan wajen bincike ko mu'amala da duk wani jirgi maras matuki. 

Kungiyar ta IS dai ta fito da wannan sabon salon yaki ne a daidai lokacin da take kara fuskantar matsin lamba daga sojojin Iraki a kokarinsu na neman kwato birnin Mosul daga hannunta.  

A watan Oktoban da ya gabata mayakan Kurdawa biyu suka halaka a yayin da wasu sojojin Faransa biyu suka jikkata a lokacin  da wani jirgi mai sarrafa kansa da Kungiyar IS ta dana wa bam ya tarwatse a garin Irbil na kusa da birnin Mosul.