1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargabar koma bayan arzikin duniya a bana

Gazali Abdou TasawaFebruary 18, 2016

Cibiyar Nazarin Tattalin Arzikin Duniya ta Turai ta OCDE/OECD ta ce faduwar farashin man fetur da ma'adanai na iya yin mummunan tasiri ga tattalin arzikin duniyar a shekara ta 2016.

https://p.dw.com/p/1HxOs
Russland russisches Geld und Sparbuch
Hoto: DW/E. Samedowa

Cibiyar Nazari da Hasashen Tattalin Arzikin Duniya ta Turai ta OCDE/OECD ta bayyana fargabar yiwuwar tattalin arzikin duniya ya fuskanci matsala a shekarar bana. A cikin wani rahoto da ta fitar a wannan Alhamis kungiyar ta ce tattalin arzikin duniya zai bunkasa ne da kashi uku daga cikin dari kawai a shekarar bana akasin hasashen da ta yi na farko a watan Nuwamban da ya gabata da ke cewa zai karu da kashi 3,3 cikin dari.

Kungiyar wacce ke da cibiyarta a birnin Paris ta ce tana fargabar faduwar farashin man fetur da na wasu ma'adanan karkashin kasa da ma koma bayan tattalin arzikin da Chaina take fuskanta su iya yin mummunan tasiri ga tattalin arzikin duniyar a wannan shekara.

Kungiyar ta ci gaba da cewa matsalar koma bayan tattalin arzikin ta bana za ta zamo ruwan dare kasancewa akasin yadda a baya karfin tattalin arzikin wasu manyan kasashe ya taimaka ga rage kaifin matsalar, a bana babu wata kasa daya da ke da wani karfin da zai iya ba ta damar daukar wannan nauyi.