1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargabar kisan kare dangi a Bangui

Ahmed Salisu
August 24, 2017

Wannan gargadi na MDD na zuwa ne daidai lokacin da jama'a ke ganin dakarun Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da kawayensu sun gaza magance rikicin, yayin da a share guda kungiyoyin bada agaji na kasa da kasa suka fara gajiya.

https://p.dw.com/p/2img2
Zentralafrikanische Republik Proteste und Gewalt in Bangui
Hoto: picture-alliance/AA/H.C. Serefio

Majalisar Dinkin Duniya ta ce muddin ba a tashi tsaye wajen magance rikicin da ake yi a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ba to lamarin na iya rikidewa zuwa kisan kare dangi kan wasu kabilu na kasar.

Rikicin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya dai na cigaba da yin kamari don ko a 'yan kwanakin da suka gabata Musulmi da Kiristoci da ke zaman doya da manja da juna sai da suka yi artabun da ya kai ga zubar da jini. Jama'a a sassan kasar da dama na zaman dar-dar yayin da masu rajin kare hakkin dan Adam ke cewar irin yadda ake keta alfarmar dan Adam a wannan kasa abu ne da ba zai musaltu ba.

Zentralafrikanische Republik UN Soldaten
Hoto: Getty Images/AFP/P. Pabandji

Baya ga 'yan kasar da ke ji a jika sakamakon wannan rikici da ya ki ci ya kuma ki cinye, a share guda kungiyoyin bada agaji da ke aiki a kasar sun ce lamarin fa na shafarsu domin ma'aikatansu da dama sun ce ba za su iya cigaba da aiki ba. Wannan ne ma ya sanya gamayyar irin wadannan kungiyoyi suka aikewa babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteres wasika inda suke korafi kan irin halin da su da ma sauran jama'a ke ciki.

Lewis Mudge na kungiyar kare hakkin dan Adam ta HRW ya ce ko kusa ba sa muntanta  dan Adam. Irin laifukan yakin da ake aikatawa ba za su musaltu ba, wannan shi ya sa da dama suka damu. Yanzu ya ragewa dakarun Majalisar Dinkin Duniya duk da rashin yawansu na su gaggauta samar da yanayi da za a yi sulhu tsakanin kungiyoyin da ke rikici da juna sannan a hukunta wanda ke da hannu wajen kashe-kashen da aka yi kana a fara shiri na raba 'yan bindiga da makamansu.

Yayin da Lewis Mudge ke wadannan kalamai, a shere guda masu sanya idanu kan rikicin wannan kasa na ganin shawo kansa da karfin tuwo ba zai yiwu ba matukar ba a kai ga datse hanyoyin da kungiyoyi masu dauke da makamai ke samun kudade ba. Guda kuwa daga cikin wannan hanya ita ce hakar lu'u-lu'u wanda ke zaman ma'adanin da Allah ya albarkaci kasar da shi.