1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fargabar IMF game da Pakistan

Hukumar lamuni ta Duniya ta nunar da cewa ambaliyar ruwa da Pakistan ke fiskanta zai jawo rauni ga tattalin Arzikinta.

default

Hukumar lamuni ta Duniya ta bayyana fargabarta dangane da illar da ambaliyar Ruwa ka iya haifar ma tattalin arzikin ƙasar Pakistan. Kakakin IMF ya bayyana wa manema labarai cewa, bala'in da Pakistan ke fiskanta zai yi tasiri akan harkokinta na zuba jari. Jami'in bai bayyana ko hukumarsa za ta dakatar da shirin da ta tanada na taimaka ma tattalin arziki Pakistan murmurewa ba.

Amma ya ce ƙasar na ɗaya daga cikin inda 'yan kasuwa da sauran masu hannu da shuni ba su da sha'awar zuba jari  a yanzu. Ita dai hukumar ta lamuni ta yi alkawarin bai ma Pakistan bashin miliyon dubu da ɗari daya na dalar Amirka idan ta cika sharuɗan da ta gindaya mata.

Aƙalla mutane 1600 ne suka rasa rayukansu a bala'in ambaliyar ruwa da ƙasar  ke ci gaba da fiskanta; ayayin da wasu ƙarin miliyon biyu suka rasa matsugunansu sakamakon ruwan sama mai yawan gaske da aka shafe kwanaki goma ana yi a ƙasar ta Pakistan.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Zainab Mohammed Abubakar